Amurka Ta Dage Haramcin Mu'amala Tsakanin Jami'anta Da Na Taiwan

Sakataren Harakokin Wajen Amurka Mike Pompeo

A jiya Asabar sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce zai dage takunkumin mu’amala tsakanin jami’an Amurka da takwarorin su na kasar Taiwan, wani matakin da zai fusatar da China kana ya kara tankiya tsakanin Beijing da Washington a kwanakin karshe na mulkin shugaban Donald Trump.

China tana ikirarin kasar Taiwan mai bin tafarkin dimokaradiya, mai cin gashin kanta cewa yankinta ne, kana tana kwatanta Taiwan da muhimmin batu ga alakarta da Amurka.

Yayin da Amurka kamar kowace kasa bata da wata mu’amala a hukumance da Taiwan, gwamnatin Trump tana kara bada goyon baya ga kasar dake kan tsibiri da sayar mata makamai da dokoki da zasu taimakawa Taiwan din ta tinkari matsin lambar China.

A wata sanarwa, Pompeo ya ce shekaru da dama ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta haramta mu’amala tsakanin jami’an diflomasiya da sojoji dama wasu jami’an Amurka da takwarorin su na Taiwan.

Ya ce “gwamnatin Amurka ta dauki wannan maki ne bisa shawara, a wani yunkurin kwantar da hankalin gwamnatin kwaminisanci a Beijing,” inji Pompeo a wata sanarwa.

Ya ce “a yau ina sanar da cewa zan dage wannan takunkumi da muka aza da kan mu”.