Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutun 300,000 Suka Kamu Da COVID-19 a Rana Guda a Amurka


Ranar Asabar 9 ga watan Janairu cibiyar samar da bayanan cutar coronavirus ta Jami’ar Johns Hopkins ta bada rahoton cewa mutane kusan miliyan 90 suka kamu da cutar ta coronavirus a fadin duniya.

Amurka ta fi kowacce kasa adadin wadanda suka kamu da cutar inda ta samu kusan mutun miliyan 22 da suka kamu da cutar. Daga nan sai India mai kusan adadin mutun miliyan 10.5.

A jiya Juma’a mutane sama da 300,000 suka kamu da cutar, wani adadi na tarihi da aka gani a Amurka.

Yayin da cutar ke yaduwa a wasu jihohin Amurka, shugaba Joe Biden mai jiran gado ya ce ya yarda da raba riga kafin cikin sauri ta yadda duk mai bukata zai samu. 'Yan makonni daga baya za a bada zagayen riga kafin na biyu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG