Jakadan Amurka a kasar Zimbabwe Brian Nicholas yace wajibi ne Zimbabwe ta dukufa wajen gudanar da sauye-sauye masu ma’ana muddin tana son Amurka ta cire wa manyan jami’an ta takunkumi.
Jakadan dai yayi wannan furucin sailin da ya ziyarci shugaban kasar Emerson Mnangagwa a fadar gwamnatin kasar dake birnin Harare.
Ziyarar ta tsawon sa’a guda tazo ne, sati guda bayan da shugaban Amurka Donald Trump yasa hannu a wata dokar gyara demokaradiyya da inganta tattalin arzikin kasar Zimbabwe wanda ake kira ZIDERA.
Dokar dai ta sake sabunta takunkumin ne da Amurka tasa wa wasu mutanen kasar ta Zimbabwe dama wasu kanfanin ta, tun daga shekarar 2002.
Shima shugaban na yanzu Emerson Mnangagwa na cikin wanda wannan takunkumin ya shafa.