Yanzu haka kasar Zimbabwe na cikin zaman kila wa kala domin ko an jinkirta rantsar da sabon shugaban kasar da aka zaba ranar talatin ga watan jiya.
Hakan ko ya biyo bayan kalubalantar sakamakon zaben da aboki karawar zababben shugaban kasar yayi ne a kotu.
Wannan dai shine zaben farko da kasar tayi cikin sama da shekaru da yawa ba tare da sunan tsohon shugaba Robert Mugabe ba a katin jefa kuri’a.
Masu kula da al’amuran siyasa su kansu sun kasa tantance wannan hali da kasar ta tsinci kanta a halin yanzu.
Wakiliyar Muryar Amurka daga kasar Africa ta kudu Anita Powel ta aiko da rahoton cewa sati biyu Kenan da kammala zaben wanda aka bayyana shugaban dake kan gado Emerson Mnangagwa wanda ya karbi ragamar mulki daga Robert Mugabe bayan yayi murabus amma har yanzu ba a rantsad dashi ba.
Sai dai masu ido na kasashen duniya sun yaba da yadda zaben ya gudana domin ko sunce anyi shi cikin kwanciyar hankali da lumana.
Sai dai kuma a waje daya sun bayyana shakkun su akan yadda yanayin runfunar jefa kuri’arsuka kasance dama yanayi a lokacin yakin neman zabe.
A zamanin mulkin tsohon shugaban Mugabe dai duk lokacin da aka yi zabe ana iya hasashen sakamakon, domin ko ansha sukan sa da kwarewa wajen aringizon kuri’a da kuma yiwa masu jefa kuri’a barazana.
Facebook Forum