Kakakin rundunar shiga Tsakani na Amurka a yankin Col John Dorrian, a jiya Laraba ya kira yunkurin Turkiya na sanarwa tare da shirya ayyukan rundunar hadin gwiwa da mai rauni, a lokacin da yake yiwa manema labarai na helkwatan sojin Amurka ta Perntagon ta hoton bidiyo, yace wannan ba tsari bane mutum zai yi tunanin gani daga abokin aiki.
Yace sun samu labari kasa da sa’a daya kafin gudanar da wannan farmakin. Wannan ba isasshen lokaci ne da za a iya yin wani abu ba a cewar Dorrian daga Bagadaza.
Dorrian ya kara da cewar ba mu san inda ainihin za a kai wannan farmakin ba kuma ba lokaci ne da rundunarmu zasu iya daukar wani mataki ba. Yace sojojin Amurka suna kimanin kilomita goma kacal daga inda farmakin ya auna.
Dorrian ya caccaki Turkiya game da tasirin wannan farmaki a kan kokarin murkushe kungiyar IS a Syria, mataki da ya ta’allaka a kan rundunar Kurdawa da suke fada karkashin rundunar hadin gwiwar Syrian Democratic Forces ko kuma SDF.