Mahalarta zaman sauraron jawaban sun samu damar yin tambayoyi game da wadanda ke rukunin tsaron shugaban kasa, kuma sun samu fahimta kan batutuwa da dama game da batun kawar da barazana daga Korea ta Arewa, abin da wani babban jami’I na gwamnati ya kira babbar masifa, wadda gwamnatin shugaba Kim Jong Un marar natsuwa ta ke haddasawa.
Da karfe goma sha biyu na rana duka sanatoci dari suka tattaru a ginin gwamnati dake kusa da fadar White House, inda aka musu jawabai, inda sakataren tsaro Jim Mattis da abokan aikinsa sakataren harkokin waje Rex Tillerson da darektan ma’aikatar tattara bayanan sirri da kuma babban hafsin hafsoshi General Joseph Dunford suka jagoranci zaman tattaunawar.
Shugaba Donald Trum ya halarci zaman tattaunawar kuma ya kira wannan zaman mai muhimmanci.
Ko shakka babu an yi tattaunawa mai natsuwa inda muka fahimci matakai da ake dauka da kuma shirin matakan soji idan bukatar haka ta taso da kuma dabarun diplomasiya wanda ya fahimtar dani dabarun sun yi daidai da barazanar, inji Sanata Chris Coons na jami’iyar Democrat kuma shugaban kwamitin huldan kasashen waje a majalisa a lokacin da yake yiwa manema labarai bayani bayan taron.
Facebook Forum