"Manufofin kasashen waje sune na cikin gida haka zalika manufofin cikin gida sune na kasashen waje," inji mai bada shawara a kan tsaron kasa Jake Sullivan yana fadawa masu zaman sauraron sa ta yanar gizo.
“Yakama mu dauki matakan da zamu karfafa kan mu domin magance matsalolin da muke huskanta a fadin duniya,” inji Sullivan. Ya ce “yanzu haka, babban kalubalen tsaron kasa dake gaban Amurka shine ta maida hankali ta gyara harkokinta na cikin gida.
A hali da ake ciki kuma, ‘yan majalisa da dama a Amurka a cikin wannan lokaci sun fuskanci barazanar tsaro, yayin da kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi ta yi kira ga karin jami’an tsaro a majalisun dokokin kana ta yi zargin cewa ba hadari jama’a kadai suke fuskanta ba har da abokan gaba na cikin majalisar kanta.
Kalaman Pelosi na ranar Alhamis na haska batun karuwan tankiya tsakanin jami’iyun siyasa a majalisar a kan damuwar kare lafiyar su, tun bayan hari a kan majalisar a cikin wannan wata da magoya bayan tsohon shugaba Donald Trump suka yi. Mutum biyar ne suka mutu a cikin tarzomar.
Sama da ‘yan majalisa 30 suka sanya hannu a kan wata wasika a wannan mako dake kira ga karin tsaro a gundumomin su. Suna masu fadin cewa barazana a kan ‘yan majalisa na karuwa ainun a cikin ‘yan shekaru, inda aka samu barazana dubu hudu da 900 a karshen shekarar kudi a watan Satumban shekarar 2018.
Rundunar ‘yan sanda a majalisar dokokin Amurka ta ce tana daukar matakan kare ‘yan majalisar yayin da zasu je da dawowa aiki, a cewar wani sakon imel da shugaban ‘yan sandan majalisar ya aike, wanda kamfain dillancin labaran Associated Press ta bankado a jiya Juma’a.