A yau Litinin Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya ce ya na goyon bayan a hukunta wadanda suka yi yunkurin juyin mulki a Turkiyya, sai dai ya yi gargadin cewa ya kamata gwamnati ta yi taka-tsantsan domin kada ta wuce gona da iri, yayin da ta ke kokarin maido da doka da oda.
“Muna tare da gwamnatin Turkiyya,” amma kuma muna kira ga gwamnatin ta Turkiyya da ta kwantar da hankulan mutanen kasar baki daya.” In ji Kerry bayan wata ganawa da ya yi da takwarorinsa na kungiyar tarayyar turai a Brussels.
Kerry ya kuma yi kira ga gwamnatin da ta bi tsarin doka na mutunta cibiyoyin dimokradiyya, inda ya kara da cewa lallai su suna goyon bayan a hukunta masu laifi, amma kuma kada a wuce gona da iri wajen hukunta masu hanu a yunkurin juyin mulkin.
Kafofin yada labarai mallakar gwamnati sun ruwaito cewa ya zuwa yanzu an dakatar da jami’ai 8,777 kana ana tsare da wasu 6,000 daga bangaren shari’a da na soji, bayan yunkurin juyin mulkin na ranar juma’a, lamarin da ya sa kasashen duniya suka nuna ya kamata a yi taka-tsantsan domin kada a ruguza ginshikan da suka tsaida doka da oda a kasar.