Amurka, Slovenia Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Fasahar 5G

Shugaban Slovenia, Borut Pahor (dama) da Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo (Hagu)

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da takwaran aikinsa Anze Logar na Slovenia, sun rattaba hannu kan wata matsaya da aka cimma wacce ta shafi sabuwar fasahar samar da hanyar sadarwar intanet ta 5G.

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Morgan Ortagus ta ce yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattaba hannu akai a yau Alhamis ta “nuna muhimmacin tsaron fasahar ta 5G – a tsakanin kungiyar tsaro ta NATO da kungiyar tarayyar turai ta EU.

Cikin wani sakon Twitter da ta wallafa, Ortagus ta ce, “kasar Slovenia ta shiga jerin kasashen da suka himmatu wajen yin kandagarki ga sha’anin tsaronsu, da kare bayanan sirri da fasahohinsu.

Ziyarar ta Pompeo a kasar ta Slovenia, ita ce ta farko da wani Sakataren harkokin wajen Amurka ya kai tun bayan 2011.

Daga cikin ayyukan da zai yi a yau Alhamis a kasar, akwai ganawa da Frai Ministan Slovenia da kuma shugaba Borut Pahor.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce daga cikin muhimman batutuwa da za a tattauna akai akwai batun samar da makamashin nukiliya, da kuma hadin kan yankin Balkan.