"Yayin da sabuwar gwamnati ke kama madafun iko a Washington, ina so ka fahimci cewa, muna tare da kai da kuma al’ummar Japan dari bisa dari, Mr. Firai Minista." In ji Mattis.
Mattis ya bayyana haka ne yayin ganawa da Abe a lokacin tafiyarsa ta farko tunda ya zama shugaban ma’aikatar tsaron Amurka.
Abe ya yaba ziyarar ta Mattis da ya kai, yayin da shugaban kasar ta Japan yake shirin kai ziyara Washington a mako mai zuwa.
Kasancewa sakatare Mattis ya zabi gabashin Asiya da Japan su zamanto kasashen da ya kai ziyararsa ta farko a kasashen ketare, ya nuna yadda gwamnatin Amurka ta dauki dangantakarta da Japan da muhimmanci.
A daya bangaren kuma, Mattis ya bayyana cewa za a maida martani yadda ya kamata idan Korea ta arewa ta kaiwa Amurka ko kuma abokan kawancenta harin nukiliya.