Ya kara da cewa babu tababa kan cancantarsa.
Trump yace ya gayawa Amurkwa lokcin da yake yakin neman zabe cewa zai nemo alkali da ya fi cancanta a duk fadin kasar. Yace tarihin alkali Gorsuch da irin shaidar karatunsa da suka hada da digiri daga jami'o’in Columbia daHarvard, basa misaltuwa. Kana yayi digirin digirgir a jami’ar Oxford dake Ingila
Daga nan shugaban yayi kira ga 'yan Democrats da Republican a majalisar dattijai, wacce tilas sai ta amince da zabensa, su hada kai "ko da sau daya domin ci gaban kasa."
Da yake magana Alkali Gorsuch yace zuwa kotun koli, "yana daga cikin ayyuka mafiya nauyi da daukaka a gareshi." Yace idan har majalisar dattijai ta amince da nadinsa zai yi bakin kokarinsa na zama "mai mutunta tsarin mulki da dokokin wannan babbar kasa."
Idan har aka amince da shi,Gorsuch zai kasance alkalai a kotun kolin Amurka mai mafi karancin shekaru-watau 49. Shine zai maye gurbin mai shari'a Antonin Scalia, shima mai ra'ayin mazan jiya, wanda ya rasu bara.
Sai dai shugaban marasa a rinjaye a majalisar dattijai Chuck Schumer, yace tilas ne alkali Gorsuch ya nuna cewa "shi ba dan gani-kasheni na masu ra'ayin rikau ba ne.
Shi kuma shugaban masu rinjaye Mitch MCconnell ya yaba da zaben da Mr.Trump yayi.