Fadar shugaban Amurka ta White ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta binciki irin rawar da Iran take takawa a rikicin da ake yi a Yemen, tana zargin Iran da assasa rikicin domin ta kara fadada burinta na mamayar yankin.
Saudiyya, abokiyar kawancen Amurka, ta zargi Iran da samar da makamai ga 'yan tawayen Houthi, ciki harda makami mai linzami, da saudiyyar ta tare, bayan da aka auna tashar jirgin samanta a Riyadh.
Saudiyya ce jagorar gamayyar rundunar hadin guiwa dake fafatawa da 'yan tawayen Houthi, a zaman goyon bayanta ga gwamnatin kasar, har ta fada a farkon makon cewa, matakin na Iran ana iya kallonsa a zaman "ayyana yaki akan kasar."
Sanarwar da fadar ta shugaban Amurka ta bayar a yau laraba, ta bayyana goyon baya ga kasar Saudiyya da wasu kawayenta a yankin, tana mai cewa Iran ta keta haramcin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi mata na raba makamai.