Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Farmaki Ta Sama Ya Hallaka Mutane 26 A Yemen


Rikicin Yemen ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 10,000 ya kuma haddasa matsalar taimakon jinkai.

Jami’an kiwon lafiyar kasar Yemen sun ce an kashe akalla mutane 26 a wani hari ta sama da jiragen saman yaki suka kai a arewa maso yammacin kasar.

Harin ta sama da aka kai yau Laraba ya shafi wani Otel da kuma wata kasuwa dake makwabtaka da shi a lardin Saada, wanda ke kusa da iyakar kasar da Saudi Arabia.

‘Yan tawayen Houthi, da suke rike da babban birnin Yemen shekaru 3 da suka wuce, sun dora laifin akan hadakar dakarun da saudi ke jagoranta akan kai harin ta sama.

Kungiyoyin kare hakkokin bil’adama sun zargi dakarun hadin guywar da kai harin Bom a unguwarnin fararen hula tun lokacin da suka fara kai farmakin su don taimakawa gwamnatin Yemen da kasashen duniya suka amince da ita a watan Maris na shekarar 2015.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG