Trump ya amsa tambayoyin manema labarai a kan batutuwa da dama a jiya Juma’a da rana, ciki har da batun matakan da Amurka zata dauka a kan kasar ta Venezuela.
Venezuela na fama da matsaloli inji Trump, yana mai cewa, babu wutar lantarki ba mai da motoci zasu yi aiki da shi a kasar. Yace idan kana tunanin bin tafarkin gurguzu ne, to ka dubi kasar Vebnezuela.
Tun da safiyar jiya ne manzon Amurka na musamman a Venezuela, Elliott Abrams, yace sakataren harkokin wajen Mike Pompeo yana rike da jerin matakan da akwai yiwuwar daukar su, ciki har da takunkuman tattalin arziki domin kasancewar sojojin Rasha a Venezuela.
Jiragen yakin Rasha guda biyu sun isa wajen birnin Caracas a ranar Asabar waccan mako kuma ana zaton akwai sojojin Rasha da kayan aikin su a cikin jiragen.