Hukumomin cikin gida da na kasashen waje da ke ayyukan ba da agajin gaggawa a Mozambique, na ta ayyukan taimakawa wadanda guguwar Idai ta raba da muhallansu, yayin da suka fara fuskantar wata babbar matsala – wato matsalar barkewar cutar amai da gudawa ko kuma kwalara.
Wani babban jami’in kiwon lafiya Ussene Isse, ya fadawa manema labarai a jiya Laraba cewa, an samu mutum biyar da suka kamu da cutar a wani yankin birnin Beira da ke gabar ruwa.
Beira shi ne yankin da guguwar ta mai kaca-kaca a lokacin da ta ratsa ta kasar ta Mozambique Malawi da Zimbabwe a makon da ya gabata.
Guguwar dai ta daidaita matattarar ruwan da ke shayar da birnin na Beira.
Susan Makuza, na daya daga cikin mazauna wani kauye da ake kira Shona, wanda shi ma guguwar ta shafa.
Ta ce “Makomar rayuwarmu na cikin hadari, saboda ba mu san me za mu yi ba, a da muna samun abinci, amma yanzu babu.”
A halin da ake ciki, kungiyar likitoci ta kasa da kasa ta Doctors Without Borders, ta dukufa wajen kulawa da mutanen da suka kamu da cutar ta kwalara, tare da daukan matakan dakile yaduwarta.
Facebook Forum