Amurka Na Shirin Kakabawa Rasha Takunkumi

'Yan Majalisun Tarayyar Amurka na shirin hukunta kasar Rasha da wasu takunkumi saboda katsalandan din da tayi a zaben Amurka.

Wata kungiya ta jagororin Majalisar Tarayyar Amurka ta dukkan jam'iyyu ta cimma matsaya kan sabbin takunkuman da za a kakaba ma Rasa, saboda katsalandan din da ta yi a zaben Shugaban kasar Amurka na 2016, da kuma wani tanajin da zai hana Shugaba Donald Trump duk wani yinkuri na saukaka takunkumin da aka kakaba ma Rashar.

Majalisa ta gabatar da wannan kudurin dokar mai taken Yadda Za A Taka Ma Iran Burki Kan Aika-Aikarta tun sama da wata guda da ya gabata, kudurin ya kuma kunshi sabbin jerin takunkumin da aka kakaba ma Iran saboda gwajegwajen makamai masu linzami da ta ke yi.

To amma zuwan kudurin dokar Majalisar Wakilai ke da wuya, sai ya gamu da matsalolin gabatarwa. Haka zalika, Majalisar Wakilan na kuma so ta kara da tanada tsauraran takunkumai ma Koriya Ta Arewa saboda shirinta na nukiliya.

Jiya Asabar, masu wakiltar jam'iyyun awurin tattaunawar sun ce sun gayara matsalar tsarin gabatarwar, sannan sun kara tsauraran takunkuman da ake so a kakaba ma Koriya Ta Arewar.

Da alamar kudurin ya zama doka kafin hutun Majalisar Tarayya a watan Agusta.