Yanzu haka gwamnatin kasar Amurka na fuskantar gabatowar wa’adin ranar Juma’a na samar da kudaden da za a tafi da kimanin rubu'in ma’aikatun gwamnati, a kokarin kauce ma sake rufe wasu ma’aikatun gwamanti, bayan kawo karshen rufe ma'aikatun da aka yi na lokaci mafi tsawo a tarihi na kwanaki 35 a watan jiya.
Har yanzu musabbabin takaddamar shi ne batun samar da kudin gina shamaki a kan iyakar kudancin Amurka da Mexico, inda shugaba Donald Trump yake neman dala biliyan 5.7.
A daya bangaren, ita kuma jam’iyyar adawa ta Democrat ga dukkan alamu ke shirin tayin amincewa da wani adadi amma kasa sosai da abin da Shugaba Trump ke bukata.
Wasu daga cikin ‘yan majalisa sun fada a karshen satin da ya wuce cewa sun kusa cimma yarjejeniya, duk da ba a san abin da Trump zai amince da shi ba ne.