Amurka na Gargadin Hari Akan Legas

Kasar Amurka ta gargadi ‘yan kasarta dake Legas akan wani shirin kai hari akan daya daga cikin Otel din Sheraton biyu dake kusa da birin, babbar cibiyar kasuwanci a Najeriya, mai jawo masu zuba jari kuma bata fama da tashe-tashen hankula.

A wata sanarwa akan shafinta, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka tace “wadanda ke shirin aikata wannan abu nada alaqa da kungiyoyin ta’addanci,” amma bata bada Karin bayani ba.

Najeriya na cigaba da fama da tashe-tashen hankula, tun bayan barkewar rigigimu da kungiyar da aka fi sani da Boko Haram shekaru biyar da suka wuce. Harin baya-bayannan a kusa da babban birnin Tarayyar na saka an tsaurara matakan tsaro, gabannin Taron Tattalin Ariziki na Duniya da za’a gudanar daga ran 7 zuwa 9 ga watannan na Mayu.

“Zuwa watannan na Afrilu, kungiyoyi masu alaqa da ta’addanci sun shirya harin da basu bayyana taka-mai-mai inda zasu kaishi ba, amma Otel din Sheraton dake kusa da birnin Ikko zasu kaiwa harin,” a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Juma’arnnan.

“Babu wani karin bayani akan wanne a cikin Otel biyu na Sheraton ne ake shirin kaiwa harin ba, kuma babu wani karin bayani akan lokacin da za’a kai wannan hari, da yadda za’a gudanar dashi.”

Najeriya na fama da matsalolin tsaro, inda ta'addanci, da rigingimun kabilanci, da satar mutane suka fara yawaita, saboda haka ne shugaban Kasa a karshen makon jiya ya gudanar da wani taro na musamman da duka shuwagabannin tsaro, dana al-umma, dana addinai domin yanke shawarar hanyar fita daga wannan matsala.

Alhamis dinnan, wani Bom ya kara tashi a unguwar Nyanya dake birnin na Abuja, kusa da inda Bom na farko ya tashi kusan makonni uku kennan. Hare haren biyu sunyi sanadiyar rayuka sama da 90 da jikkata sama da 160.