Amurka Da Rasha Sun Shirya Tafka Muhawara A MDD Kan Batun Girke Makaman Nukiliya A Sararin Samaniya

A yau Laraba ne Amurka da Rasha za su yi jayayya kan batun kai makamin Nukiliya a sararin samaniya a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda zai kada kuri’a kan wani kudiri da Amurka ta gabatar wanda ke kira ga kasashen da su hana gasar kai makamai a sararin samaniya.

WASHINGTON, D. C. - Ana ganin Rasha za ta dakile daftarin kudurin, in ji wasu jami'an diflomasiyya. Matakin na Amurka dai ya zo ne bayan da ta zargi Moscow da kera makamin nukiliyar da za su sanya a sararin samaniya, zargin da ministan tsaron Rasha ya musanta.

Linda Thomas-Greenfield

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, da jakadan Japan na Majalisar Dinkin Duniya, Yamazaki Kazuyuki, sun bayyana a wata sanarwa ta hadin gwiwa a ranar Juma'a cewa, sun shafe makonni shida suna tattaunawa da mambobin kwamitin sulhu kan rubutun daftarin.

Rubutun ya tabbatar da wajibcin da ya rataya a wuyan kasashe na yin biyayya ga yarjejeniyar sararin samaniya tare da yin kira ga kasashe "da su ba da gudummawa sosai ga manufar yin amfani da sararin samaniya cikin lumana da kuma hana tseren kai makamai a sararin samaniya."

Yarjejeniyar sararin samaniya ta 1967 ta hana wadanda suka sa hannu kan yarjejeniyar da suka hada da Rasha da Amurka kai abubuwa "falakin duniya, duk wani abu da ke dauke da makaman nukiliya ko duk wani nau'in makaman kare dangi."

Rasha da China na shirin fara gabatar da gyara ga kuri'ar da aka kada a majalisar. Gyarar ta yi daidai da shawarar 2008 da su biyu suka yi na yerjejeniyar hana "duk wani makami a sararin samaniya" da barazana "ko amfani da karfi a kan abubuwan sararin samaniya."

Ba a sa ran za a amince da gyarar ba, in ji jami'an diflomasiyya. Gyarar da daftarin kudurin kowanne yana bukatar a kalla kuri'u tara na goyon baya sannan kuma babu wata kuri'a da Rasha, China, Amurka, Birtaniya ko Faransa za su amince da ita.

-Reuters