Amurka Da Rasha Sun Cimma Dai-daituwa Akan Makamai Masu Guba Na Siriya

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov.

Amurka da kasar Rasha sun amince akan wani shiri dangane da kasar Sham ko Siriya, na tabbatarwa ta kawar da makamanta masu guba, a ciki harda gabatar da takarda mai lissafe da duka makaman Syriya masu guba a cikin mako daya.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bayanna shirin a wata ganawa da yayi da takwaran nasa na Rasha Sergei Lavrov a gaban manema labarai a birnin Geneva yau Asabar.

Your browser doesn’t support HTML5

Kalaman Sakatare Kerry Akan Siriya - 0:18


Kerry yace "Mun kai ga amincewa akan adadi da ire-iren makamai masu guba da gwamnatin Assad ta mallaka, kuma zamu cigaba da mayar da himma wajen gani kasa da kasa ta kwace ikon wadannan makamai."

Kerry yace sun amince cewa dole sai Syria ta bada damar a bincike duka wuraren da ake ajje wadannan makamai, wadanda yace za’a lalata amma ba a cikin Syria ba.

Ya kara da cewa idan Syria bata amince da wannan shiri ba, to zasu iya nemo izinin amfani da kuduri na 7 a kundin kwamitin tsaro na MDD, wanda ya bada damar ayi amfani da karfi.

Sai dai takwaran nasa yace shirin bai tanadi komai ba akan ko za’a yi amfani da karfi.

Wannan yarjejeniya da aka cimma a halin yanzu, ta zone bayan tattaunawar kwanaki uku tsakanin manyan-manyan jami’an diflomasiyya da jakadan kungiyar kasashen larabawa dangane da Syria, Lakhdar Brahimi.

Wannan shiri dai da aka tanadar, zai iya kawar da harin sojin Amurka a Syria, domin mayar da martani akan cewa wai gwamnatin Syria tayi amfani da makamai masu guba akan fararen hula a watan da wuce daura da birnin Damascus.

Amurka tace ta tabbatar sama da mutane 1,400 ne suka mutu a harin, kuma babu shakka sojojin Syria su ne suka kai wannan hari. Gwamnatin Assad dai tace a’a, ba ita bace, ‘yan tawaye ne suka tabka wannan ta’asa.

Kamfanin dillacin labaran kasar Faransa, yace wani jami’an Amurka ya gayawa manema labarai a birnin Geneva cewa ta iya yuwuwa akwai wurare 45 da dake da alaqa da shirin makamai masu guba na kasar Syria.

Daga gefe daya kuma, A jawabinsa na mako-mako, Shugaban Amurka Barack Obama yace sahihiyar barazanar sojin Amurka na daga cikin dalilan da suka sa aka samu yiwuwar masalahar diflomasiyya da zai raba kasar Syria da makamanta masu guba.

Shugaban yace Rasha ta nuna wani sabon yunkuri na shiga sahun sauran kasashen duniya wajen matsa wa Syria ta rabu da makamanta masu guba, irin wandanda aka yi amfani da su a watan da ya wuce suka yi sanadiyar rayukan Syriawa sama da dubu 1.

Mr. Obama yace gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad taki amincewa tana da makamai masu guba mako guda da ya wuce, amma yanzu ta yarda.

Shugaban yace Sojojin Amurka zasu cigaba da jira a kusa da Syria, har sai kasar da yankin gabas ta tsakiya ta bada makamanta masu guba.

Ibrahim Alfa Ahmed na Muryar Amurka ya tattauna da masanin harkokin siyasar duniya, Farfesa Buba Namaiwa.

Your browser doesn’t support HTML5

An Cimma Dai-daituwa Tsakanin Amurka Da Rasha Akan Syria - 3:09