Amurka Da Koriya Ta Arewa Sun Ce Za Su Gana

Manzon Koriya ta Arewa Kim Yong Chol poses da Donald Trump

Za ayi ganawar da aka shirya yi tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un, ranar goma sha biyu ga watan Yuni a Singapore.

Shugaban Amurka ne ya bayyana haka jiya a fadar White House, bayanda ya karbi wasika daga Kim da wani babban jami’I mai shiga Tsakani kan batun makaman nukiliya na kasar Koriya ta Arewa ya mika mashi hannu da hannu.

Bayan ganawa ta ba sabanba da tsohon jami’in ma’aikatar leken asirin Koriya ta Arewa a fadar White House, shugaba Trump ya sanar da sake komawa kan shirin taron kolin da shugaban Koriya ta Arewa Kim Joung Un.

Bayan ganawa ta sama da sa’a guda, shugaba Trump ya sanar da cewa dukan bangarorin biyu sun mance da musayar kalamai masu gauni da aka yi a lokutan baya, da suka kai ga jingine ganawar da ake shirin yi.

Koriya ta arewa tana neman dama a fannin harkokin tattalin arziki da kuma sassaucin takunkuman da aka kakaba mata da suka durkusar da kasar.