Amurka da kawayenta na neman a kara kakabawa Koriya ta Arewa takunkumi

Ashton Carter sakataren tsaron Amurka

Amurka da kawayenta, na ingiza mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, domin ganin an kada kuri’a cikin gaggawa kan kudurin kara takunkumi akan kasar Korea ta Arewa.

Takukumin zai ba da damar a yi bincike kan kowane irin kaya da za a shigar kasar da kuma dakatar da wanda za a fitar, wadanda ake tunanin za a iya yin amfani da su wajen hada makaman soji.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Samantha Power, ta gabatar da kudurin a jiya Alhamis, makwanni bakwai bayan wata ganawa da aka yi tsakanin Amurkan da China, wacce kawace ta kut-da-kut ga Korea ta Arewa.

A wani mataki na nuna karfin kariyar da ta ke da shi idan aka harba mata makamamin nukiliya, a jiya Alhamis Amurka ta harba wani makami mai linzami daga sansanin sojin ta da ke California, wanda ya doshi Tsibirin Marshall da ke kudancin tekun Pacific.

Akalla ire-iren wadannan gwaji na makamai masu linzami 15 Amurka ta yi, tun daga watan Janairun shekarar 2011