Amurka Da Isra'ila Na Kai Ruwa Rana

Shugaban Amurka Barack Obama da PM Isra'ila Benjamin Netanyahu

Bayan da Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sake lashe zabe, dangantaka tsakanin kasar da Amurka na kara tsamari.

Shugaban Amurka Barack Obama, ya gayawa Firaministan Isra’ila Benyamin Netanhayu cewa zai yi nazarin dangatakar da ke tsakanin Amurkan da Isra’ila, bayan kalaman da Firai Ministan ya yi na cewa bai amince Falasdinu ta zama kasa mai cin gashin-kanta ba.

A cewar wata majiya a Fadar White House, a jiya Alhamis ne Mr Obama ya gayawa Firai Ministan hakan, a lokacin da ya kira shi domin ya taya shi murnar lashe zabe kasar da aka yi.

Gabanin gudanar da zaben ne Mr Netanyahu ya ce ba zai taba yadda Falasdinu ta zama kasa mai cin gashin-kanta ba, a matsayin neman hanyar sasanta rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu.

Har ila yau a jiya Alhamis, ya gayawa kafofin yada labaran Amurka cewa bai ki a kwance damarar yakin Falasdina ba, inda ya kara da cewa amma hakan, ya na ganin ba abu ne mai yiwuwa a yanzu ba.