Da alamun Amurka da China zasu sanya hanu kan yarjejeniyoyin cinikayya a lokacinda shugaban Amurka Barack Obama da shugaban Sin Hu Jintao zasu yi taron kolinsu cikin makon nan a Washington.
Da alamun Amurka da China zasu sanya hanu kan yarjejeniyoyin cinikayya a lokacinda shugaban Amurka Barack Obama da shugaban Sin Hu Jintao zasu yi taron kolinsu cikin makon nan a Washington.
Akwai kuma yi yuwar Shugabannin kasashen mafiya girman tattalin arzikin Duniya zasu tattauna kan batututwa da dama da suka shafi tattalin arziki,amma guda mafi muhimmanci shine gibin cinikayya tsakanin kasashen biyu inda a bara China take da rarar dala milyan dubu metan d a 70.
Ana jin ‘yarjejeniyoyin zasu hada da cinikin jirage,kayan motoci,kayan amfani gona,da kuma naman dabbobi ga China. Haka kuma ana jin za’a cimma yarjejeninoyi kan sabbin hanyoyin samar da makamashi da danginsu.