WASHINGTON, DC —
Yau Talata Frai ministar Burtaniyya Theresa May da shugaban Amurka Donald Trump sun nuna alamun yiwuwar fadada dangantakar cinikayyar dake tsakanin kasashen biyu a yayin da suka fara wani zama a birnin London.
Da yake magana a wani zauren tattaunawa akan harkokin kasuwanci, Trump ya ce yana tunanin kasashen biyu zasu cimma muhimmiyar yarjejeniyar cinikayya wadda zata amfane su.
Ita kuma May ta ce, ta yiwu Burtaniyya da Amurka su fadada dangantakar tattalin arzikin su ta hanyar cimma yarjejeniya, kuma gwamnatin ta yarda da barin kofofin kasuwanci a bude kuma ba tare da wani shinge ba.
Trump ya nemi cimma yarjejeniyar kasuwanci da wasu manyan kasashe kawayen Amurka, ciki harda China, da zummar cimma sharuddan da zasu amfani Amurka.