Amurka Ce Ta Fara Sanar Da Faransa Rasha Ta Yi Mata Kutse

Adiral Mike Rogers

A jiya Alhamis ne wani jami’in tsaron ‘kasa na Amurka, ya fadawa ‘yan Majalisa cewa Amurka ta sanar da jami’an Faransa cewa Rasha ta yiwa hanyar sadarwar kwamfutocin Faransa kutse lokacin da ake gudanar da zaben shugaban ‘kasa, tun kafin kowa ya sani.

Daraktan hukumar tsaron Amurka, Admiral Mike Rogers, yace “muna sane da abin da Rasha ta ke yi a lokacin zaben Faransa, wanda ya faru a ‘yan makonnin da suka gabata. Ya fadi haka ne alokacin da yake bayar da ba'asi gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan bayanan sirri, yace “Mun yi tunananin abu ne mai muhimmanci da har muka tuntubi takwarorinmu na Faransa muka sanar da su.

Hukumar kanfen ‘din zaben Faransa ta fada tun ranar Asabar cewa “a kwai bayanai masu yawa,” wanda wasunsu na bogi ne, kan ‘dan takarar shugaban ‘kasa mai tsaka-tsakin ra’ayi, Emmanuel Macron, inda aka yada bayanan a kafofin sada zumunta.

Bayanan dai sun bayyana awowi 36 kafin ‘karshe na ranar Lahadi, wanda Macron ya doke abokiyar takararsa Marine Le Pen.

Jami’an hukumar zaben Faransa sunce bayanan da aka kwarmata, sun fito ne daga wata kwamfuta da ke dauke da sakonnin email ‘din Macron da na wasu daga ciki manajojin kamfen dinsa.