"Amurka ta dawo," shelar da Biden ya yi kenan a Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, a babban jawabinsa na farko kan manufofin harkokin waje, a matsayinsa na Shugaban kasa. "Amurka ba za ta iya janye kanta daga al'amarin duniya ba. Manufofin harkokin wajenmu sun ginu ne kan diflomasiyya."
Ya ce "Kawanceceniyar da Amurka ke yi ne babban jarinmu," a yayin da ya ke kuma gargadi ga Rasha da China kan kudurin Amurka. Trump, wanda ya yi amfani da taken, "Saka Amurka a farko," ya sha yin baran baran da dadaddun kawayen Amurka.
Biden ya ce ya gaya ma Shugaban Rasha Vladimir Putin, ta wayar tarho a makon jiya cewa "Lokacin da Amurka ke mirgina gaban Rasha ya wuce." Game da China kuma, Biden ya ce, "Za mu yi aiki da China, a duk lokacin da ya kasance da amfani gare mu."