Amurka Ta Lissafa Ayyukan Haifar Da Tarnaki Da Iran Ke Yi

Ofishin jakadancin Amurka da ke Majalisar Dinkin Duniya, ya ce Jakadiyar Amurka a majalisar, Nikki Haley, za ta yi amfani da wani taron manema labarai a yau Alhamis “domin zayyana ire-iren ayyukan haifar da tarnaki da Iran ke yi a yankin Gabas Ta Tsakiya” da sauran sassan duniya.


Jakadiya Haley, za ta yi bayani game da wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan yadda aka cimma matsaya dangane da shirin mallakar makamashin nukiliyan Iran da kasashen Amurka, Burtaniya, China, Faransa, Rasha da kuma Jamus.


Matsayar ta kuma amince da kada Iran ta gudanar da aikace-aikacen hada makami mai linzami, wanda da za a iya dasa makamin nukiliya akansa.
Wasu bayanan farko da aka fitar gabanin wannan taron manema labarai da za ta gabatar, sun nuna cewa Jakadiya Haley, za ta karanto wasu “hujjoji kwarara” da ke nuna cewa Iran ba ta mutunta wannan yarjejeniya, sannan ta yi kokarin bat da sahun wasu ayyukanta.


Dama dai shi shugaba Donald Trump, bai amince da wannan yarjejeniya ba, wacce tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya kulla, a matsayin hanya madaidaiciya da za ta hana Iran mallakar makamin nukiliya.