AMURKA: An Yi Macin Cika Shekara Daya da Kashe Wani Bakar Fata a Ferguson

Jiya 'Yansandan Ferguson suna bin masu zanga zangar tunawa da kashe Michael Brown shekara daya da ta wuce

Bakake sun yi macin tunawa da Michael Brown bakin fata matashi da wani dansanda farar fata ya harbe a Ferguson dake jihar Missouri shekara daya da ta gabata

‘Yan sanda a birnin Ferguson da ke Jahar Missouri a Amurka, sun ce wani mutum guda yana cikin mawuyacin hali, bayan da jami’an tsaro suka harbe shi a musayar wutar da aka yi, yayin da masu zanga zangar lumana ke macin cika shekara guda da kisan da wani dan sanda farar fata ya yiwa wani bakar fata matashi da ba ya dauke da makami.

Shugaban ‘yan sanda karamar hukumar St. Louis, John Belmar, ya ce ‘yan sandan farin kaya sun kasance sun sakawa wani mutum ido, wanda suka yi fargabar ya na dauke da makami, wanda kuma ya shiga wata musayar wuta da aka yi tsakanin wasu kungiyoyi biyu da aka harba harsashai 40 zuwa 50, kafin daga baya ya bude wuta akan motar ‘yan sandan wacce ba ta da alama.

Hakan ya sa suma ‘yan sanda fararen kayan suka mayar da martini lamarin da ya ka da shi.

Jaridar St. Loius mai suna Dispatch, ta ruwaito mahaifin mutumin ya bayyana sunansa a matsayin Tyrone Harris Junior mai shekaru 18, wanda ya kasance amini ne ga Michael Brown mai shekaru 18 da ‘yan sanda suka kashe a Ferguson a bara.

Sai dai shugaban ‘yan sandan, ya ce wannan harbi, cikas ne ga ci gaban da ake samu, yana mai jaddada cewa, masu zanga zangar ba su da hanu a wannan harbi.