Masu rajin kare ‘yancin bil’adama da malaman addini ne suka yi cincirundo mafi yawancin su bakaken fatar Amurka a birnin da ya fi yake dauke da mafi yawancin bakaken fata. Macin da aka yi shi karkashin jagorancin mahaifi da sauran iyalan mamacin Micheal Brown dan shekaru 18 a duniya.
Mutuwarsa a ranar 9 ga watan Agustar bara ya tada bore na tsawon kwanaki a birnin. Daga baya kuma aka ci gaba da zanga-zangar watannin bayan masu yanke hukunci sun ki bawa farar fatar dan sanda laifin kisan kan.
Ana zaton yau Lahadi, yawan jama’ar zai karu, a inda za su taka salin-alin har zuwa Coci don yin bauta tare da addu’oi. Mahaifin Micheal Brown ya fadawa manema labarai a jiya Asabar cewa, zai yi iyakar kokarinsa don raya mutuwar dansa saboda ceton ‘yan baya.
Sannan wasu zasu yi tsit na tsawon minti 4 da rabi, a matsayin girmamawa ga sa’o’I 4 da rabi da shi Micheal Brown yayi a mace bayan an harbeshi akan titi kafin a dauke gawarsa.