Rundunar ‘yan sandan New York ta kori wani dan sanda farar fata, wanda ya shake wani bakar fatan da ya kama a shekarar 2014 har ya mutu, batun da ya kai ga zanga-zanga a fadin kasar.
Kalaman bakar fatan mai suna Eric Garner, yayin da ya ke goshin mutuwa, wato “Ba na iya numfashi,” sun zama abin yawan ambato ga masu zanga-zangar, wadda ta haifar da muhawara a fadin kasar kan batun jinsi da kuma yawan amfani da karfin da ya wuce kima da ‘yan sanda ke nunawa.
Wannan ya sa aka kafa kungiyar rajin kare bakaken fata ta “Black Lives Matter,” wato ran bakake ma na da muhimmanci.
Kwamishinan ‘yan sandan New York, James O’Neill, ya fadawa ma manema labarai jiya Litini cewa an kori jami’in dan sanda, Daniel Pantaleo, daga aiki ne saboda mutuwar Garner.
Ya ce sallamr ta biyo bayan shawarar da wani alkalin rundunar ‘yan sandan ya bayar kwanan nan.