Fitattun tsoffin 'yan wasan kwallon kafa na Super Eagles a Najeriya, Daniel Amokachi da Joseph Yobo, sun mika sakon fatan alherinsu ga dan wasan Najeriya Ahmed Musa, wanda ke shirin komawa kasar Saudiyya da taka kwallo.
A shafin Instagram na @ahmedmusa718, Amokachi da Yobo, suka shiga suka mika sakonninsu.
"Barka! Allah ya ba da sa'a, bisa wannan sabuwar himma da ka sa gaba." Inji @danielamokachi.
Shi kuwa @jyobo234, wanda ya taba rike kambun kyaftin na Super Eagles, cewa ya yi, "barka abokina, ina mai maka fatan alheri."
A Jiya Asabar, Musa, wanda shi ya fara ciwa Najeriya kwallayenta biyu a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Rasha, ya wallafa jawabin godiya da ban-kwana ga kungiyarsa ta Leicester City a shafinsa na Instagram na "ahmedmusa718."
"Ina son na mika godiya ta ga kowa da kowa a kungiyar Leicester City da suka sani farin ciki yayin dan takaitaccen zama na a Ingila."
Ya kara da cewa "wannan kungiya ta taimaka min na cimma burina na buga wasa a gasar Premier - ko dan wannan, ina mai matukar mika godiya ta."
Akalla masu bibiyar shafin Musa na Instagram 1,914 (a lokacin rubuta wannan labari) suka shiga suka yi tsokaci.
Yayin da wasu ke taya shi farin ciki, wasu kuwa cewa suke bai yi dabara ba lura da cewa, yana kan ganiyar tashensa zai koma kasar ta Saudiyya.
Musa zai zamanto dan wasan Najeriya da ya fi kowa tsada cikin 'yan wasan kasar da ke buga kwallo a kasashen waje.