Amnesty International Ta Ce An Sanar Da Sojoji Kafin A Sace 'Yan Matan Dapchi

Makarantar Dapchi inda aka sace 'yan mata 110

Sakamakon binciken Amnesty International ya nuna cewa an sanar da sojoji fiye da awa hudu lokacin da 'yan Boko Haram suka shiga garin amma basu dauki wani mataki ba lamarin da kakakin sojojin ya musanta kana shi ma Alhaji Bello Arabi ya yi shakkar abun da sojojin suka fada

Mai magana da yawun kungiyar Amnesty International a Najeriya Malam Isa Sanusi ya yi bayani akan sakamakon nasu binciken dangane da yadda kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan Dapchi daga makarantarsu.

A cewarsa jama'an garin sun sanar da hukumomi fiye da awa hudu cewa 'yan Boko Haram sun shiga garin . Mutane sun yi tsammani cewa mahukumta zasu dauki matakin tunkararsu amma basu yi ba har suka kwashe 'yan matan. Ya ce sai da 'yan ta'addan suka tafi da 'yan matan sannan jami'an tsaro suka isa makarantar.

Kungiyar Amnesty ta kira gwamnati da ta yi binciken kwakwaf ta gano sahihin gaskiyan abun da ya faru. Injishi bai kamata a ce kasa da take da dokoki da tsaro a ce wasu sun shiga makaranta sun kwashe yara ba.

Amma da yake mayar da martani kakakin hedkwatar sojojin Najeriya Birgediya Janar John Agim ya ce zargin ba gaskiya ba ne. A cewarsa babu yadda za'a ce an sanarda sojojinsu da batu mai mahimmanci a ce basu yi komi ba. A ganinsa Amnesty International bata nufin Najeriya da alheri saboda shugaban kasa ya kafa kwamiti mai karfin gaske ya binciki lamarin. Ya ce kwamitin bai ma fitar da sakamakon bincikensa ba sai gashi kungiyar ta fitar da nata. Ya ce kokari ne na wofantar da binciken kwamitin gwamnati.

Janara Agim ya ce a lokacin da lamarin ya faru babu sojoji a garin domin tun makonni shida da suka gabata sojoji suka bar garin hannun 'yan sanda yayinda su kuma suka nufi garin Kanamma mai iyaka da Jamhuriyar Nijar domin kai dokin gaggawa.

Amma daya daga cikin dattawan jihar Yobe Alhaji Bello Arabi Sardaunan Damaturu ya yi shakkar abun da sojojin suka fada. Ya ce ko ta ina bai yadda da bayanin ba domin babu hujjar janye sojoji a yankin.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Amnesty International Ta Ce An Sanar Da Sojoji Kafin A Sace 'Yan Matan Dapchi - 2' 54"