Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Kai Ziyara a Dapchi


Buhari In Dapchi
Buhari In Dapchi

A karon farko shugaban Najeriya Mohmmadu Buhari ya kai ziyara jihar Yobe, inda ya jaddada matsayar gwamnatinsa kan aikin da take yi na ganin an ceto ‘yan matan makarantar Dapchi.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa za a samo ‘yan matan Dapchi 110 da aka sace.

Da yake magana a wani taro da ya hada da jami’an gwamnatin jihar Yobe da shugabannin tsaron Najeriya da kuma shugabannin addinai, shugaba Buhari ya bayyana nasarar da gwamnatinsa ta yi na ceto wasu daga cikin ‘yan matan da aka sace a baya.

Haka kuma shugaban ya fadawa mahalarta taron cewa gwamnatin Najeriya ta hada gwiwa da sauran kasashen waje ciki har da makwabtan kasar domin tabbatar da ganin an samo ‘yan matan Dapchi cikin koshin lafiya.

Shugaban ya yi gargadi kan cewa za a hukunta duk wani da aka samu da kawo katsalandan a aikin ceto ‘yan matan.

“Na umarci hafsohin soja da sufeto janar na ‘yan sanda da su jagoranci aikin ceton, su kuma sanar da ni halin da ake ciki kullum,” a cewar shugaba Buhari.

Shugaban ya sha alwashin gwamnatinsa za ta tsaya tsayin daka wajen yaki da ta’addanci da kuma kungiyar Boko Haram.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG