Amirka tayi Allah wadai da hoton vidiyo, wanda bisa dukkan alamu ya nuna wasu sojojin kundubalam Amirka suna yin fitsari akan gawarwarkin mayan kungiyar Taliban.
Jiya Alhamis sakataren tsaron Amirka Leon Panetta yace hoton vidiyon abin yin tir ne. Ya kuma lashi takobin cewa za'a hukunta wadanda keda alhakin aikata wannan aikin asha.
Leon Panetta ya baiwa rundunar sojojin kundubala da shugaban jami'an tsaron kungiyar kawancen tsaro ta NATO a Afghanistan umarnin sun binciki al'amarin.
Itama sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton tabi sahin sakataren tsaron Amirka wajen yin tir da hoton vidiyon.
Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan yace gwamnatinsa ta damu sosai da wannan hoton vidiyon daya baiyana da zaman cin mutunci ne.
Ma'aikatar tsaron Amirka, wadda ake cewa Pentagon a takaice tace bata da wani dalilin tababan sahihancin hoton vidiyon.
Jiya Alhamis jami'an Amirka suka ce rundunar sojojin kundubala ta gano ko su wanene sojojin da suka aikata wannan akili, to amma ba'a baiyana sunayensu ba.
Shi ma kwamanda rundunar sojoji kundubala Janaral James Amos yace ya bukaci sojojin kundubala da mayakan ruwa su gudanar da nasu binciken akan al'amarin.
Hoton vidiyon dai ya nuna sojojin kundubala sanye da unifam suna yin fitsari akan gawarwarki guda uku.