Amfani Da Tsarin Addinan Najeriya Zai Iya Taimakawa Sabbin Shugabanni Masu Zuwa - Malamai

taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

Yayin da ya rage kasa da mako uku sabbin shugabanni su karbi ragamar mulki a Najeriya, malaman addini na ganin akwai bukatar a daura shugabannin bisa ga tafarkin da za su samu nasarar shugabanci.

Wannan na zuwa ne lokacin da har yanzu Najeriya ta kasa fita daga matsalolin rayuwa da suka addabi sassa daban-daban na kasar, duk da shekaru da aka kwashe ana samun shugabanci.

Tun daga lokacin da Najeriya ta kasance kasa ‘yanci ta samu jagoranci daga shugabanni daban-daban, kama daga na mulkin soji har zuwa farar hula, sai dai har yanzu ta kasa fita daga matsalolin rayuwa wadanda ke yi wa ‘yan kasa tarnaki.

Wasu ‘yan kasar na dora alhakin kasancewar kasar cikin wannan yanayi ga shugabancin da ta ke samu, kuma hakan ba ya rasa nasaba ga yadda suke ganin akwai bukatar malaman addini su kusanci sabbin shugabanni da za su karbi ragamar mulki da shawarwari, don neman samun mafita ko rage matsalolin da kasar ke fuskanta.

Farfesa Mansur Ibrahim Sakkwato, malamin addini musulunci ne a Najeriya da ke cikin masu wannan ra'ayin, ya ce malaman addini sun jima suna neman su samu shugabanni wadanda za su saurari shawarwari na gaskiya, domin a samar da mafita daga matsalolin.

A hauji mabiya addinin krista ma koyarwar addinin ta bukaci shugabanni da su nemi samun hikimar gudanar da mulki daga wurin Allah, don hakan ne kadai zai sa su samu nasarar shugabanci.

Raberan Yakubu Oro, malamin addinin krista ne a Najeriya ya bayar da misali da annabi Sulaimanu, wanda ya nemi hikimar gudanar da mulki daga wurin Allah.

Ya ce ko yanzu idan shugabanni za su nemi hikimar gudanar da mulki daga Allah, za su samu nasarar mulkin su ba tare da matsala ba, ya kuma ceto Najeriya daga cikin yanayi na tabarbarewa da take ciki a halin yanzu.

Sau da yawa, ‘yan siyasa wadanda suka bayar da gudunmuwa wajen dora gwamnati kan yi wa masu mulki kane-kane wajen rabon mukamai, shi ma Farfesa Mansur ya ce musulunci ya tanadi yadda shugabanni ya kamata su yi.

Yanzu dai ya rage kasa ga mako uku sabbin shugabanni su fara jan ragamar shugabanci, kuma wasu daga cikin su suna samun shawarwari sai dai aiki da shawarwarin ne kan iya nuna ko za su yi tasiri ko akasin haka.

Domin Karin bayani ga rahotan Muhammad Nasir.

Your browser doesn’t support HTML5

Amfani Da Tsarin Addinan Najeriya Zai Iya Taimakawa Sabbin Shugabanni Masu Zuwa - Malamai - 3'27"