Hakan na zuwa ne yayin kaddamar da wata Manhaja ta bayanan sirri mai suna Intelligence Application System ko IRS a takaice, wadda ake sa ran za ta samar da sahihan bayyanai da rahotani kan tsaro ga gwamnati da al’umomin kasa.
A na kallon wannan ci gaba ne da aka samu ta fannin kimiya, da ya kai ga kirkirar wannan Manhajar IRS, don samar da sauki a hanyoyin shawo kan matsalolin tsaro a Najeriya, da makwabtanta da ke fuskantar matsalar rashin tsaro, a cewar shugaban kamfanin samar da tsaro na Beacon Security Consultant wanda a karkashinsa aka kirkiro da manhajar Kabiru Adamu.
La'akari da mahimmancin bayanan sirri wajen yaki da rashin tsaro a kasa, Abubakar isa, daya daga cikin matasan da suka samu horo wajen fahimtar yanayin amfani da sabuwar fasahar, ya ce Manhajar za ta bayar da bayanan tsaro na hakika ga jami'an tsaro da 'yan Najeriya
Yan Najeriya dai na ganin shigar da kimiya da fasahar zamani za su taimaka wajen rage aukuwar ayyukan bata gari da ke addabar sassan kasar da dama.
Najeriya dai na daga cikin kasashen da suka rugumi kimiya da fasaha, sai dai a wannan lokacin da kasar ke shirin gudanar da manyan zabukanta a shekarar 2023, yan kasar na kira da a inganta fannin don rage yawan hare- hare na miyagun iri dake haifar da koma baya ga duk wani ci gaba da ya shafi kasar.
Domin Karin bayani saurari rahotan Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Your browser doesn’t support HTML5