Wata babbar kotun kasashen Turai ta zartar da hukunci akan wata makaranta dake kasar Jamus, a dalilin karya doka da tayi na daukar hoton wani kamfani da wallafa shi a shafin makarantar.
Hoton da yake nuna daliban makarantar na gudanar da wani aikin makaranta, wanda suka dauki yaran zaune da malaminsu a gaban kwamfuta, daga bisani makarantar ta bada hoton da akayi amfani da shi a shafin makarantar na yanar gizo, kuma aka wallafa hoton batare da neman izinin wanda ya dauki hoton ba.
Kotun tace mutane na ganin shi a matsayin wani abu da bashi da muhimanci sosai, kotun ta ayyana cewar makarantar na bukatar neman izinin wanda ya dauki hoton kafin amfani da shi a kowane mataki.
Madaukin hoton Dirk Renchhoff, ya tabbatar da cewar ya baiwa kamfanin sufurin izinin daukar hoton sa, amma ita makarantar bata tuntubeshi ba kafin daukar hoton.
Don haka yake karar makarantar da neman a biya shi tarar kudi da suka kai kimanin Naira dubu dari biyu, kotun ta bukaci makarantar da ta biya shi wadannan kudaden kana da gujema aiwatar da irin wannan aika aika a gaba.