Ayayin da ake kwanaki kadan ga watan zulhija lokacine da maniyyata daga dukanin sassan duniya ke tururuwa zuwa kasar saudiya domin gudanar da aikin hajji, bisa al’ada alhazai da suka isa kasar saudiya da wuri na fara zuwa madina ne domin gudanar da ziyararsu.
Al’ada dai ta nuna cewa duk wanda suka je umrah ko aikin hajji ana zuwa gabatar da ziyara da ibada da kuma ganin wuraren tarihi inda baki kanje, kuma ana wannan ziyara ne ta hanyar hada kai a dauki shatar mota guda domin zagayawa domin bude ido.
Sai dai abin sha’awa shine wani jagoran tafiya ziyara wanda Harami ke ya dauki nauyin haka ta hayar anfani da daliban kasashen daban daban domin yi wa kasar su hidima --Jibril Muhammad Arabi, dalibi a jami’ar Madina na daya daga cikin jagororin Nijeriya, a madina ya kuma bayyana yadda suke gudanar da wannan ziyara.
Ya ce suna fuskantar matsaloli daga tsofaffi da wadanda suke da karancin waya wajen fahimtar da su yadda zasu gudanar da ayyukansu tare da nuna masu hanyoyin da suka dace domin tabbatar da basu bata ba.
Your browser doesn’t support HTML5