Al’ummar unguwar kofar kaura dake cikin garin Lafia, a gabar wani kogi sun shaida cewa, tuni ambaliyar ta hallaka rayuka uku yayinda kayayyaki da dama suka salwanta.
A cikin hira da Muryar Amurka, mazauna yankin sun bayyana cewa galibinsu talakawa ne, wadanda basu da halin sake gina wani matsuguni, suka kuma nuna irin hadarin dake tattare da ci gaba da zama a wurin da suka ce tamkar zama a bakin ramin mutuwa ne, suka kuma nemi taimakon gaggawa daga gwamnati da suka bukaci ta saye gidajen ta samar masu wani matsuguni.
A nashi bayanin gwamnan jahar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa, babban abinda ya ke kawo ambaliyar ruwa a wurare da dama shi ne yawan zubar da shara a magudanun ruwa da ke toshe hanyar ruwa. Ya kuma sanar da sake dawo da tsarin yin shara kowanne karshen wata don yashe magudanan ruwa.
yankunan-jihohin-adamawa-da-taraba-sun-fara-fuskantar-ambaliyar-ruwa
hukumomi-sun-yi-kashedi-a-kan-ambaliya-a-kano-da-makwabtanta-
A nata bangaren, hukumar agajin gaggawa NEMA a shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya, wadda alhakin kula da wadanda irin wannan bala’in ya aukawa ya rayata a wuyanta ta bayyana cewa, banda agazawa wadanda lamarin ya shafa, suna fadakar da al’umma kan matakan kare kai daga ambaliyar.
Ko a cikin watan Satumba, an fuskanci mummunan ambaliyar ruwa a jihar Kogi sakamakon gocewar da tekun Naija ya yi, wanda ya kwashe gonaki da gidajen daruruwan mutane, ya kuma tafi da motoci da dama da ke tafiya kan hanya.
Hukumomi da kwararru sun yi gargadi da cewa akwai yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a jihohi da dama na Najeriya da kuma wadansu sassan kasashen Afrika.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5