Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Yiwu a Samu Ambaliyar Ruwa a Wasu Yankunan Najeriya - NEMA


Ambaliyar ruwa
Ambaliyar ruwa

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya da ake kira NEMA ta yi gargadin yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa a wasu kananan hukumomi fiye da 100 a Najeriya.

A cikin wata sanarwar da shugaban hukumar NEMA, AVM Muhammadu A Muhammed ya fitar, hukumar ta shawarci mazauna yankunan da su yi kaura domin tsira da rayukansu da kuma dukiyoyinsu.

Kananan hukumomin da ake hasashen aukuwar ambaliyar sun hada da Kaura, Zaria, Kaduna North da ke jihar Kaduna, sai kuma jihohin da ke yankin kudu maso yammacin kasar da tuni har sun fara fuskantar matsalar ambaliyar.

Ambaliyar Ruwa a Birnin Lagos
Ambaliyar Ruwa a Birnin Lagos

Wasu daga cikin mazauna birnin Lagos sun nuna damuwarsu, kuma sun yi kira ga hukumomi da ma mazauna yankunan da su fito a hada hannu da karfe wajen shawo kan wannan matsalar.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG