Ambaliyan Ruwa Ya Yi Barna A Jamhuriyar Niger

Ambaliyan ruwa a Jamhuriyar Niger

Hukumomin jamhuriyar Niger sun baiyana irin barnar da ambaliyar ruwa ta haddasa daga lokacin da aka fara samun ruwan sama zuwa ranar 6 ga watan Agusta.

Gidaje 3131 ne suka rushe a yankunan da ambaliyan ruwa ya afkawa daga farkon daminar bana zuwa farkon watan da muke ciki na Agusta. Ruwan ya lalata gonakin da fadinsu ya kai kadada 3902. Ministan ayyukan jin kai Alhajin Lawan Magaji yace abbobi 26344 ne kuma suka hallaka a sanadiyar wannan al’amari da ya lalata rijiyoyi 33 da wasu dakunan karatu 11 da suka rushe

Ya zuwa ranar 6 ga watan nan na Agusta Jihar Maradi ce ke kan gaban jihohin da wannan bala’ai ya afkawa inda aka kiyasta cewa mutane 19,549 suka rasa muhallansu. Sai jihar Diffa inda matsalar ambaliya ta rutsa da mutane 9064 yayinda mutane 6798 ke cikin irin wannan hali a jihar Zinder. Amma ministan ya ce gwamnatin ta tsara shirin tallafawa dukkan wadanda suka rasa mahallansu..

Domin kaucewa barkewar cututtuka dake da nasaba da matsalar ambaliyan ruwa gwamnatin ta Niger tace ta tanadi isassun magunguna da gidajen sauro.

A saurari rahoton Souley Mamman Barma

Your browser doesn’t support HTML5

Ambaliyan Ruwa Ya Yi Barna A Jamhuriyar Niger – 2’ 43