Hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta ce mutum 100 su ka riga mu gidan gaskiya a jihohi 10 na Najeriya. Ambaliyar ruwar ta fi barna a jihohin Niger da Kogi a arewacin Nigeria, sai kuma jihohin Anambra da Delta a kudu maso kudu da kudu maso gabashin Nigeria.
Baya ga dalilin yawan ruwan sama da kan kawo ambaliyar ruwan, kwararre kan yanayi da gine-gine injiniya Muhammad Bello ya ce rashin bin ka’idar tsara birane na ta’azzara lamarin. Yace su san mahimmancin bude magudanan ruwa da kuma gyarasu idan lokaci ya yi. Ya yi kashedin cewa a daina yin gine gine akan magudanar ruwa. Gwamnati kuma ya kamata ta tabbatar an tanadi magudanar ruwa kafin mutane su soma gine gine.
Muhammad Usman Madaci dan jihar Jigawa a arewa maso yammacin Najeriya ya baiyana damuwar yadda ambaliyar ta shafi garin nan mai albarkar noma na Auyo da gefen Kafin Hausa. Baya ga share gonaki ambaliyar ta katse hanyoyin mota a yankin.
Idan ba’a mance ba, shugaban hukumar hasashen yanayi ta Najeriya Farfesa Abubakar Mashi ya yi bayani filla-filla kan yadda damuna za ta kasance da ambaliyar ta ba zata. Yace akwai wasu matsalolin irinsu tsawa da yadda ruwan ke da yawa a cikin takaitaccen lokaci wanda ke haddasa samun ambaliya.
Rahotanni sun baiyana cewa ambaliyar ruwan bana a Najeriya ta fi ta kowace shekara tsanani.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5