Rayuwa a wuraren da ake hako karfen uranium tayi ma mutanen wurin wuya saboda yawan rashin lafiya da suke samu tare da yawan mace-mace.
Zasu kai karar kamfanin dake hakar karfen gaban majalisar dokokin kasar domin a shafe masu hawaye ta tilastawa kamfani ya dauki matakan karesu.
Sun bukaci kamfanin ya kafa asusun taimako na musaman domin mutanen da suka riga suka tagayyara sakamakon gubar dake fitowa daga karfen na uranium.
Malam Almustapha Alhassan na kungiyar dake fafutikar kare muhalli yace yanzu an samu shekaru hamsin ana hako uranium a yankin amma Nijar bata ci ribarshi ba kuma uranium yana da illa da yawa saboda yana haddasa cuta da yawa. Yace akwai wani lokacin da cikin rana guda sai mutane uku su rasu.
Malam Alhassan yayi kira a natsu a yi shiri a taimaki kowa a kawo ka'idodi wadanda yakamata zasu kayyade illolin dake tattare da uranium da abun da dole sai an yi domin a kare jama'a. Saboda haka za'a kaima majalisar dokoki ta tantance ta gyara lamarin, a daidaita kuma a ajiye dalolin da za'a dauka nan da nan a yi aiki.
A nasa bangaren Malam Abdurahaman Muli magajin garin Arlit yace mai zurfin ido tun da wuri yake soma kuka. Yace lokaci ya zo da za'a tattauna a shawo kan matsalar.
Wailin gwamnati ya nuna goyon baya game da matakin da wakilan gundumar suka dauka.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5