Inji Magajin Garin Sokoto tsohon Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki ya rasu ne a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya a wajejen karfe takwas zuwa tara na yammacin jiya.
Yau za'a dauki gawar sarkin zuwa Sokoto inda za'a yi masa jana'iza bayan sallar azahar a masallacin Sultan Bello daga nan kuma a kaishi Hubbaren Shehu a binneshi.
Game da tunawa da tsohon sarkin Magajin Garin Sokoto yace marigayi Ibrahim Dasuki mutum ne mai son zaman lafiya kuma mai hazaka. Duk abun da yake ciki akan samu nasara saboda hazakarsa. Yana da basira amma duk abun da ya fi so shi ne a zauna lafiya. Yayi ayyukan gwamnati da yawa tare da shugabanci Jama'atul Nasril Islam kafin ya samu zama Sarkin Musulmi.
Alhaji Ibrahim Dasuki shi ne sarkin musulmi na farko daga gidan Buhari kuma shi ne na goma sha takwas.
Inji Alhaji Hassan Dan Baba Marafa babu wani dan sarki da ya bautawa sarautar Sokoto irin shi marigayi Ibrahim Dasuki. Yayi iyakacin kokarinsa ya bautawa sarautar kuma Allah ya taimakeshi shi ya zama sarkin musulmi.
Ga firar da Aliyu Mustapha yayi da Magajin Garin Sokoto da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5