Alkalin babbar kotun dake shari’ar kisan tsohon daraktan gudanarwa na rundunar sojin Najeriya, Manjo janar Idris Alkali, mai shari’a Daniel Longji, ya tsame kansa daga ci gaba da shari’ar saboda karancin lokacin da yake da shi.
Ganin yadda wannan shari’a za ta kwashi lokaci ya sa alkali Daniel Longji, ya cire kansa daga shari’ar saboda shirin yin ritaya da ya yi, bayan kwashe shekaru 45 yana aiki.
Babban lauya mai gabatar da ‘karan wadanda ake zargi da kisan Alkali, Joe Kyari Gadzama, ya ce an shigar da ‘kara a kotun daukaka kara dake garin Jos.
Shi kuma lauyan dake kare wadansu daga cikin wadanda ake zargi da kisan Manjo Janar Idris Alkali, Mahan Mafuyai, ya ce suna fatan wanda zai ci gaba da shari’ar zai yi iya kokarinsa wajen gudanar da shara’ar.
Shima lauyan dake kare wasu da ake zargi da kisan, Bitrus Fwangshak, cewa ya yi har yanzu ba a ma fara sauraron shaidu a karar ba.
A ranar uku ga watan satumbar bara ne Manjo Janar Idris Alkali ya bace a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja, inda daga bisani sojoji suka ce sun ga gawarsa a yankin Dura Du dake karamar hukumar Jos ta Kudu a jahar Pilato.
Domin Karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.