Ali Nuhu ya ce ya kamata 'yan kallo su rika taimaka mu su, su yi yaki da barayin fasaha
WASHINGTON, DC —
Idan ku na biye da mu kun ji hirar Halima Djimrao kashi-kashi da shahararren dan wasan fina-finan Najeriya, Ali Nuhu wanda a kwanakin baya can ya zo nan Amurka ya karbi wata lambar girma da karramawa a fannin aikin shi na yin fina-finan Hausa da aka yi bikin bayarwa a birnin New York. A karashen hirar Ali Nuhu ya ce kasuwar fina-finan Hausa wane Najeriya, ta bunkasa har a kasashen yammacin Afirka kamar su Nijer da Ghana da Kamaru. Daga nan sai Halima Djimrao ta kada baki ta ce da Ali Nuhu, kowace irin kasuwa idan ta bunkasa ta gawurta, akwai wasu matsalolin da take tafe da su wadanda sai an yi da gaske a yi maganin su, sannan ta tambaye shi ko su ma a sana'ar su suna fuskantar irin wadannan matsaloli musamman ma a kasuwannin sayar da fina-finai?
Your browser doesn’t support HTML5