Ali Nuhu ya ce ba ma zai iya kwatanta fina-finan Hausa da na wani harshe ba saboda su suka kafa shi, su ne sanadin daukakar da ya samu a duniya
WASHINGTON, DC —
Shahahararren dan wasan fina-finan Hausa Ali Nuhu bai jima da komawa gida Najeriya ba daga nan Amurka inda ya zo ya karbi wata lambar yabo da karramawa wadda ya lashe a fannin aikin shi na yin fina-finai. Jim kadan da karbar lambar yabon na tattauna da shi, kuma idan kuna biye da shirye-shiryen mu kun ji kadan daga cikin doguwar hirar da muka yi da shi, har ma mu ka tabo batun cewa baicin fina-finan Hausa har wa yau yana ya na yin na turanci da 'yan kudancin Najeriya. A ci gaban tattaunawar ta mu da Ali Nuhu, na tambaye shi, tsakanin fim din Hausa da na Turanci, wanne ya fi wuya da wahalar yi, sai ya kada baki ya amsa da cewa: