A yayin wani zaman shari’a a ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba ne alkali Okon Abang na Kotun Tarayya da ke Abuja ya bada umurnin a tsare Ali Ndume a gidan yari akan tuhumar da ake yi wa Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban Tsohuwar hukumar kula da harkokin Fansho a Najeriya wanda tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya nada a shekarar 2013, bayan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta zarge shi da halatta kudaden haram har aka tsare shi a gidan yari aka kuma kwace masa wasu kaddarori.
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar jihar Borno ta kudu ne ya tsaya wa Maina wajen bada belinsa a baya. A wata hira da Muryar Amurka, Ndume ya ce kasa kai Maina gaban Kotu ne ya sa alkalin ya bukaci a tsare shi, duk da cewa ya nemi a bashi dama ya kare kansa amma alkalin ya ki.
Ya kara da cewa matakin ya bashi mamaki saboda akwai wadanda su ka aikata laifi fiye da na Maina, Irinsu Kanu na IPOP da ya tsere daga Najeriya da kuma Sanata Eyinnaya Abaribe wanda ya tsaya mashi aka bada belinsa da har yanzu ya na nan a majalisa ba a yi masa komai ba.
Ndume ya bayyana cewa ya bada wani gidansa da ke Abuja a matsayin daya daga cikin sharuddan bada belin, ya na mai cewa kamata yayi a rike wannan gidan saboda bai ga dalilin sa a tsare shi ba kuma ba a ba lauyanshi dama ya kare shi ba duk da cewa lauyan ya nemi a basu takardun sammacin da Kotu ta tura.
“Wannan shi ne karo na biyu da aka kai ni gidan yari, a baya ma an taba yi man kazafin da ya sa aka kai ni gidan yari.”
Saurari cikakkiyar hirarsa da Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5
An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
Your browser doesn’t support HTML5