Alhazan Jihohin Borno da Taraba Sun Yi Addu'ar Neman Zaman Lafiya a Arewa Maso Gabas

alhazai

Alhazan jihohin Borno da Taraba sun gudanar da wata addua ta musamman a Saudiya domin Ubangiji ya kawo lafiya a arewa maso gabashin Najeria musamman a jihohin nan uku da suke ta fama da rikicin Boko Haram.

Alhazan sun gudanar da addu'o'in ne domin Allah ya kawo karshen rikicin Boko Haram da kashe kashen kabilanci da na addini da suka addabi jihar Taraba. Dama jihohin Borno da Adamawa da Yobe su ne suke fama da rikicin 'yan Boko Haram.

Wani Isa Muhammed yace musamman jihar Borno an samu matsalar zubar da jini da dama. Yankin arewa maso gabas yana fama da matsalar tsaro dalili ke nan suka ga ya kamata su yi addu'a ta musamman a madadin al'ummominsu. Tun da sun zo kasa mai tsarki suka ga yakamata su roki Allah.

Buhari Ahmad daga jihar Taraba yace ganin yadda abubuwa suka rincabe a jhohin arewa maso gabas tare da jihar Taraba yasa suna neman Allah ya kawo karshen matsalolin. A daina tashin hankali da kisan rai.

Baban sakataren hukumar alhazan jihar Taraba Alhaji Habibu Almasi yace addu'o'in nada faida kwarai ba wai kawai ga jihohinsu ba har da kasar gaba daya. Malamai sun zauna su yi addu'a akan irin abubuwan dake faruwa a jihar Taraba. Sun kuma gayawa duk alhazai su dinga sa jihohin cikin addu'a.

Muhammed Uztaz Mustapha na ma'aikatar harkokin addini ta jihar Borno yace yadda kowa zai yiwa kansa addu'a, kasar Najeriya tana bukatar addu'a. Malamai sun yi fadakarwa domin kowa ya san halin da ake ciki.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz

Your browser doesn’t support HTML5

Alhazan Jihohin Borno da Taraba Sun Yi Addu'ar Neman Zaman Lafiya a Arewa Maso Gabas - 3' 01"